Min menu

Pages

An tsinci gawar wasu masoya guda biyu a mace a cikin daki amma anga wuka da kuma fiya-fiya a bangaren kowanne daga cikinsu

An tsinci gawarsu su biyu a mace saidai anga wuka tare da fiya fiya kusa da gawarsu


An sami gawar wasu masoya biyu a daki, masoyan da  aka kira Emmanuel Oshiotu, mai shekara 33 da Amuka Okafor, mai shekara 25, an samesu a mace a cikin dakinsu wanda yake a Uvwie a Karamar hukumar Uvwie dake jihar Delta.

Masoya biyun an samesu cikin dakinsu dake a titi mai lamba 2,Ojigbo creascent Off sapele-Effurun road a ranar Alhamis, 25 ga watan fabrairu.

Bayanai sun nuna cewa an sami maganin kashe kwari wanda ake kira da suna “SNIPER”  da kuma wuka a kusa da gawarsu, wanda hakan ke nuni da cewa kisan kai da kaine ko kuma sun kashe junansu sune.

Wasu daga cikin makotan  marigayan sun shaidawa manema labarai cewar da karfe 5:00AM  na dare sukaji Emmanuel yana ihun neman taimako. 

Bayan an karya kofar dakin ne aka sameshi  baki nata fitar da kumfa a gefe kadan dashi kuma masoyiyarsa na kwance itama rai a hannun Allah.


 Daga nan aka daukesu izuwa Babbar asibitin warri, anan asibitin aka tabbatar da mutuwarsu baki daya.

Dan sandan dake division din warri,CSP Mukhtari Bello da sauran jami’an yan sanda sunje har asibitin sun duba gawawwakin mamatan a ma’ajiyar gawa dake asibitin na warri.

Mai Magana da yawun yan sandan jihar Delta DSP Edafe Bright ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.
 
Ga asalin bidiyon 


Comments