Min menu

Pages

Akwai yiwuwar farashin abinci zaiyi ta karuwa a Nigeria

Akwai yiwuwar farashin abinci zaiyi ta karuwa a Nigeria



Daga Bashir Abdulaziz


Akwai yiwuwar abinci zaiyi ta kara tsada idan gwamnati bata dauki mataki ba. 


A wani nazari da wannan gida na duniyar labari yayi ya gano cewa akwai yiwuwar farashin abinci bazai sauko ba koda kuwa ana shigo da abincin daga kasashen ketare.


Akwai dalilai karfafa na wannan batu Wanda gaba daya sun ta'allakane da matsala ta sare bishiyoyi ko gandun daji, hakika wasu zasuyi mamakin yadda za'a ce sare bishiyoyi ne zai jawo matsalar tsadar abinci.


Aduk lokacin da bishiyoyi suka karanta ruwan sama ma zai karanta wannan kowa ya sani (kamar cikin sahara), idan kuma ruwan sama ya karanta to abincin da ake nomawa a cikin gida zaiyi karanci saboda karancin ruwan sama. A inda matsalar take shine a kowane lokaci har yau har gobe mutane a Najeriya basu daina sare bishiyoyi ba, haka kuma basa shuka wasu a madadinsu.


Abincin da ake shigowa dashi daga kasashen ketare bazai taba wadatarwa ba saboda mafi akasarin abincin da ake shigowa dashi daga waje yafi na cikin gida tsada haka kuma mutanen karkara yawanci basu damu dashi ba sama da nasu Wanda suke nomawa.


 A Najeriya a yanzu haka kayan abinci na daga cikin abubuwan da suka zamewa mutane karfen kafa saboda da matukar tsadarsu kuma duk da  yawanci ma na gidane wanda ake nomawa,Wanda ake kawowa daga ketaren ma a yanzu haka sunyi karanci saboda hana kawosu da kasa tayi.


Abin dubawa anan shine idan har ruwan sama yayi karanci ba'a sami abin noma mai yawa ba, a lokaci guda kuma boda tana rufe dole ne kayan masarufi (na abinci) suyi matukar tsada.


Mafita guda daya akan wannan babbar matsala da take ta cigaba shine hukuma.


Hukumomi na kowane bangare a Najeriya dole ne suyi karatun ta nutsu domin tabbatar da cewa mutane sun daina yiwa bishiyoyi Saran karan tsaye domin taimakon rayuwar talakawa manoma.


Sannan kira ga duk Wanda ya fahimci wannan al'amari daya taimaka duk ta hanyar dazai iya wajen shuka bishiyoyi tare da hana sarewa ba bisa ka'ida ba domin ganin cewa matsalar abinci ga talakan Najeriya bataci gaba da aukuwa ba.

Comments