Min menu

Pages

Akwai iyuwar sakin daliban kagara yau inji Gumi

 Akwai iyuwar sakin daliban kagara yau inji GumiShahararren malamin nan da yake shiga jeji da tsaunuka yana yin wa'azi tare da kiran yan bindinga da suyi hakuri su daina garkuwa da mutanen da suke su koma ga Allah subar wannan sana'ar da suke, sannan kuma ya fada musu illar aikata irin wadannan munanan ayyukan a addinance.


To yau ma malamin ya fitar da sanarwar cewar akwai iyuwar yan bindingar da suka dauke daliban makarantar kagara su sake su yau.


Kuma ya baiyana cewar ba lalle bane a basu koda sisin kobo ba, saboda fahimtar juna da akayi tsakanin malamin da yan bindingar saboda nasiha da kuma wa'azin da yayi musu.


A yan kwanakin nan ne akaji labarin cewar yan bindingar sunyi awon gaba da daliban wata makaranta dake garin kagara inda shi kuma malamin ya dira a jejin a washe garin ranar da abin ya faru.


Inda akai sulhu dasu cewar zasu bada daliban ba tare da an basu sisin kobo ba wanda hakan ba karamin abin birgewa bane ace sun bayar da daliban ba tare da an basu komai ba.


A wani bangaren mutane sai yabo suke ga malamin da har yake iya shiga jejin yana yin nasiha ga yan bindingar kuma cikin hukuncin ubangiji su yadda harma su ajiye makamansu.

Comments