Min menu

Pages

Yadda giwaye ke jana'izar yan uwansu tare da zaman makoki ( tarihin halittu

 Yadda giwaye ke jana'izar yan uwansu tare da zaman makoki ( tarihin halittu)




Yanayi na mutuwa baya taba duba halin da halitta zata shiga idan ta rasa wani abokin rayuwa domin idan da zamuyi duba da irin tsarin rayuwar halittu da dama a cikin wannan duniya zamuga cewa wasu halittun gabaki daya rayuwarsu ko jin dadinsu wajen yin farin ciki ya ta'allakane da samun dan abin da zasu ci ko yin amfani bayan sun takura   rayuwar wasu halittun. Mutuwa wannan aba ce dake matukar tasiri na din-din a tsakanin halittun ban kasa, kuma koda wane lokaci idan ta fado dauka take amma cikin silar faruwar wani al'amari.  misali mutane na kama dabbobi ko suyi farautarsu ko kuma dabba tayi farautar dabba yar uwarta kamar zaki da rakumin dawa dadai sauransu. Wani lokaci dabba tana cikin rayuwarta a daji sai aje a farautota akai gidan zoo ko izuwa gidajen tarihi a ajiyesu ba tare da tunanin halin da yan uwansu zasu Shiga ba akan hakan.

Anan zamuyi dubane dangane da yadda dabbobin daji keyi idan suka rasa nasu a sanadiyar farauta ko rashin lafiya.

 Alokuta da dama zaki idan zaiyi farauta yana shigane cikin dandazon dabbobi a daji ya kama yaci harya bari, a yayin da saura kuma suke tserewa subar gawar dan uwansu anan idan yaci koshi ya tafi yabar sauran ya rube ba tare da sauran sun waiwayi gawarba Dan daukan wani mataki kamar jana'iza ko sutura ko kuma zaman makoki, abin tambayar anan shine irin wadannan dabbobi bayan tsoran da suke dashi na  kada a kamasu a cinye shin sunajin wani abu kuwa mai kama da alhini ko damuwa na rashin wannan Dan uwa nasu ko kuma shikenan ya zama tarihi? 

Anan an samu wasu dabbobi kalilan da suke nuna alhini na rashin Dan uwansu da sukayi, abin mamaki anan shine giwaye ma sun fado cikin jerin dabbobin dake zaman makoki a bisa mutuwar daya daga cikinsu harma suna gwada yi masa sutura ko jana'iza a matsayin gawa.

 


Masu Bincikice da dama sun dade suna zargin giwayen da yiwa yan uwansu jana'iza bayan sun mutu duk kuwa da cewa basu fitar da wata kwakwkwarar hujja ba ta bidiyo dake nuni da hakan. Gaskiyar maganar cewa giwaye nayiwa gawar yan uwansu jana'iza bata fito fili bane karara watakila kodan su ba halittu bane Wanda mutane ke sha'awar dauka a bidiyo sosai, duk da an samu bayanai da suke cewa masu farauta sun sha buya cikin duhuwa suna ganin yadda giwaye ke rufe gawar yan uwansu da ganyayyaki. 

Dadi da kari masu bincike sunyi karin bayani cewa sun sha cin karo da kaburburan (makwantai,kushewa) giwaye a yayin da suke bincike, domin an gano dangin giwaye suna da dabi'ar Tattara gawawwakin 'yan uwansu waje guda cikin rami daga bisani su saka musu yayi a kai su rufe su. Haka kuma kamar yadda yan Adam kan nuna damuwa ko alhini a matsayin zaman makoki ahlin giwaye ma suna zaman makoki ta hanyar nuna kasalar jiki tare da canjawar yanayinsu  a duk lokacin da suka rasa nasu, suna nuna darajantawa ga ran Dan uwansu da suka rasa cikin girmamawa.

Wannan al'amari na yadda giwaye ke nuna kulawa akan yan uwansu ya isa a kirashi da abin al'ajabi ko kuma mu kirashi da baiwa babba.



Comments