Min menu

Pages

Tafiyar ceto

             Farkon labarin



 

A wani zamani mai tsawo daya shude anyi wani sarki MAI tarin arziki,karfin mulki hade da matukar jarumtaka a kasar farisa mai suna SAIDUN NAJABI. Sarki saidun najabi ya kasance sarki mai adalci wajen kyautatawa al'ummar kasarsa ba tare da muzgunawa ba ko  zalinci wajen tauye musu hakkoki, Wannan sarki bashi da addini amma kuma yana amfani da bokaye duk da ya kasance shi baya tsafi ko kadan, kuma yana daga hujjarsa  cewa shi a nasa hangen nesan shugaba bashi da addini domin idan hakan ta faru baza'ayi adalci ba in jishi domin wata rana zai iya nuna bambamci wajen hukunci ko kyautatawa.


A bangaren jarumta kuwa wannan ba wani abune da sai anyi bincike mai tsawo ba domin ya kasance jarumin maza fasa taro wadda a tarihin kasar farisa ba'a tabayin sadauki kuma jarumin sarki kamar saba, sannan bincike ya nuna cewa babu wani sarki akaf wannan nahiya dake da ilimi tamkarsa.


Sarki saidun najabi yakasance yanada matan aure Uku wadanda allah ya alsok acehi dasu da 'ya'ya bakwai wanda biyu daga cikinsu matane sauran hudu kuwa duka mazane.sarki saidun najabi yakasance mai una matukar kulawa da soyayya tsakanin matayansa da 'ya'yansa domin duk dabara da nazarin mutum don yagano wanda yafi so to saidai yaci kasa, wanda hakan tasa kosu matan da 'ya'yan kansu a hade yake domin basu san wanda yafi so ba atsakaninsu ala tilas suka hakura.


 SHABILA itace babba daga cikin matan sarki saidun najabi kuma takasance tana da 'ya'ya uku biyu maza da mace daya.JAIHAN hine babban da ga shabila da kuma awajen sarki sadun najabi sai mai bimasa kuma samira da kuma razik dake biye da ita kuma hine karami acikin dakinsu.


 Shabila takasance doguwar mace kyakykyawa tagaban kwatance ga tarin hakuri da shiru shiru da take dashi.Wanda yasa kowa agidan sarautar kama daga kan abokananta da sauran jama'ar dake gidan sarautar suke ganin marukar girmanta a matsayin babba.

 

JAIDA'ATU itace mace ta biyu a wajen sarki da kuma shabila,jaida'atu takasance mace ma'abociyar kyau, dogon gashi,bakaken labbada kuma dogon wuya mai daukar hankali sabanin shabila,jaida'atu macace mai haba-haba da raha ga jama'a wanda hakan tasanya kowa dake gidan sarautar keganin girmanta tare da yimata biyayya domin jaida'atu takasance mace tilo wadda take da bewar sarrafa harshenta cikin magana ko a zance.jaida'atu tana da 'ya'ya biyu wanda dukkanninsu mazaje ne wato samjid da abtar.


NADIYA wadda itace matar sarki ta uku kuma karama acikin matansa nadiya takasance kyakykyawace tagaban kwatance wadda samun irinta awannan zamani abune mai matikar wahalar gaske nadiya itace wanda sarki saidun najabi yafafata kazamin yakin a gasa daya kusa yarasa rayuwarsa aneman aurenta,nadiya tana da baiwar ilimi data fahintar tunanin mutane gata da kyautatawa duk wani mutum kai intakaicemaka nadiya na iya kyautar da duk masarautar sai wane da wane ke iya yinta.nadiya takasance tana da tagwayen 'ya'ya mace dana miji wato suliha da zaffar.

Wani abu kuma dake bawa jama'ar dake wannan masarautA mamaki shine tayadda babu wadda ya taba ko jin wani abu na rashin jituwa da ya taba faruwa tsakanin wannan 'ya'ya na sarki Saidun najbi domin kowa ne daya daga cikinsu yana da kyakykyawar fahimta game da dan uwansa,kuma wannan ya samu ne ta kokarin mahaifin su wajen ganin sun hade kai waje guda cikin zaman lafiya. Saidai kuma wani abu daba za'a rasa ba shine duk inda girman alaka yakai zaka iya samun wani abu wanda kowa ya bambam tashi da dan uwansa wato dai ta halayya rin ta yayan adam kuma hakan zai iya faruwa akan kowa misali Jaihan mutumne mai karancin magana kuma gashi yanason a rika girmamashi sosai hakan tasa samira wadda ke biye dashi take ganin tamkar ya da girman kai, haka  itama samira ta kasance mai dan zafin rai da saurin hantara hakan yasa Razik bai damu da ko yaushe ya mata magana ba face ita taso, Samira ako da yaushe suna tare ita da suhila domin kasancewar su kadai ne mata a 'yayan dake gidan kuma bata da yar uwa mace sai suhilan kawai. 

A bangaren samjid kuwa wadda shi ko yauhe zaka sameshi tare da Jaihan domin sun kasance sa'annun juna ne kuma tazarar dake tsakaninsu ma sati gudane kawai shi yasa suka taso cikin abota da ra'ayi iri daya, shidai samjid gabaki dayansa mahaifiyasa jaida'atu ya biyo wajen faramfaram da jama'a gashi zaiyi wuya ka ganshi yana fushi gashi da matukar saukin kai haka zalika ko yaushe Razik yana tare dashi domin shi Razik ya kasance mutum mai marukar yawaita tambaya shikuwa samjid mutum ne wadda ke bashi hadin kai wajen amsawa. Idan kuma akayi duba izuwa Abtar da Zaffar wannan kam sai wadda ya ganin domin sun kasance babu wani abu dake iya  rabasu face barci kai wani lokacin ma a waje guda suke kwana tsabar shakuwar dake tsakaninsu.


Mu kasance daku domin ci gaban labarin sannan idan kuna son sauraron labarin audio gashi a kasa




Comments