Min menu

Pages

Da dumi-duminsa saukar Buhari Daura keda wuya ya fadi wasu abubuwa masu matukar mahimmanci.

 Da dumi-duminsa saukar Buhari Daura keda wuya ya fadi wasu abubuwa masu matukar mahimmanci.Dirar shugaban kasar Nigeria mahaifarsa ta garin Daura keda wuya ya sanar da wasu abubuwa masu mahimmanci ga duk wasu yan Nigeria.

Abinda ya fara fada shine mutanen kasar suyi hankali da wannan cutar data zo ta sarkewar numfashi, har yai kira ga yan kasa gaba daya cewar yanada kyau subi umarnin hukumomin lafiya da suka fitar na amfani da duk wasu kayayyaki da zasu taimaka wajen ganin yan kasar sun kare kansu daga kamuwa da wannan cutar sannan kuma ya sake sanar da cewa yanada kyau kowa yana amfani da facemasks domin kariya daga cutar.

Batu na biyu kuma yayi ne game da kasafin kudi na wannan shekarar inda yake cewa zai tabbatar an gabatar dashi ba tare da wani matsala ko tangarda ba, har yake cewa an baiwa kowanne shugaba umarnin yadda zasu bi abubuwan dake cikin kasafin na kudin dan tabbatar da gaskiya da kuma amana.

Sannan shugaban kasar ya sabunta takardar zama dan jam'iyar Apc sannan kuma yai kira da sauran mutane suma su sabunta nasu wanda basu dashi kuma suyi domin shiga ko kuma zama cikin jam'iyar Apc din.

Bayan haka shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kira yan Nigeria da su maida hankali sosai ga harkar noma da kiyo domin harka ce da zata kai ga kasar tudun mun tsira koda dan gaba ne, domin daga karshe mutane zasu ji dadin wannan harkar dari bisa dari domin yanzu munada kamfanoni guda 42 wanda suke samar da takin zamani a wurare guda shida a fadin kasarnan.

Sai kuma shugaban yaja hankali ga shugaban ni da sauran mutane cewar suna masa adalci a mulkinsa suna fadar alkhairi a mulkinsa suna fadar abinda yayi ba suna soki burutsu ba.

Daga karshe ya nemi yan kasa suyi addu'ar  zaman lafiya a kasa.


Comments