Min menu

Pages

Bayyanar wasu photuna na gwamnan jihar jigawa Badaru Abubakar ya gayyaci gwamna Tambuwal na Sokoto bude wani guri ya jawo maganganu da dama

 Bayyanar wasu photuna na gwamnan jihar jigawa Badaru Abubakar ya gayyaci gwamna Tambuwal na Sokoto bude wani guri ya jawo maganganu da dama.



Wani abu da yake faruwa tsakanin gwamnan jihar jigawa da wasu tawagar mutane na jam'iyar PDP ya saka mutane da dama cikin rudani, inda hakan ya jawo maganganu da surutai masu yawa a kafafen yada labarai dama bakunan mutane dake zaune kurum a layi ko unguwa.

Inda mutanen dake cikin jam'iyar Apc suka shiga tunanin me yasa mai girma gwamnan zaiyi haka amatsayin sa na kusa kuma jigo a jam'iyar, har suke ganin kamar bai dace ba yana yawan shiga ko kuma yin hulda da mutanen da ba yan cikin jam'iyar sa bane. Wasuma har tunani suke cewar ko yin hakan da yake kamar zai taba garkuwar dake jikin jam'iyar tasu ta Apc ne.

Saidai a wani bangaren wasu sun ji dadin hakan domin cewa suke hakan shine siyasa kuma abinda yayi haka ya kamata kowanne dan takara ko dan siyasa yake yi domin kawar da gaba ko sasanto tsakanin mabiya.

Ko kwanan baya an hangi gwamnan cikin ladabi da girmamawa yana gaisawa da tsohon gwamnan jihar jigawa Dr Alhaji Sule Lamido a wani guri, wanda hakan ma baiyi dadi ga mutane masu yawa ba a jam'iyar ta Apc har wasu ke cewa akwai wani abu a kasa to saidai wannan ba wata magana bace da ya kamata ai amfani da ita ba.



Kafin baiyanar wannan photo na gwamnan jihar jigawa tare da Tambuwal an dan samu wata magana daga bakin gwamnan wanda bataiwa kusan duk wani dan jam'iyar dadi ba wanda akaji gwamnan da kansa yana cewa indai Apc bata gyara alakarta ta cikin gida ba zata iya rasa kujerarta a jiharsa ta Jigawa.

Hakika wannan maganar ta tada kura sosai.

Har wasu suka shiga kokonto da tunani kala kala, dan haka da wannan photunan suka sake baiyana na gwamnan suna tare da Tambuwal sai kowa yake ta fadar albarkacin bakinsa.



Comments