Min menu

Pages

Wurare biyar a Duniya wanda jirgin sama bai isa ya wuce ta samansu ba

 Wurare biyar a Duniya wanda jirgin sama bai isa ya wuce ta samansu ba



A duniya akwai wasu wurare da jirgin sama bazai iya bi ta samansu ba kodan hadarinsu ko kuma mahimmancinsu sune kamar haka:

1) Makka: Birnin makka an hana kowane jirgi bi ta saman Ka'aba domin girmama dakin Allah da akeyin bauta a cikinsa. Hakazalika bincike ya tabbatar da wajen nada matukar nauyi duk jirgin daya bi saiya fado. Domin bin wannan doka ko a lokacin Hajji bayanai sun tabbatar da cewa domin zuwa Riyadh daga Jaddesh dole jirgi yayi zagaye.



2) Nahiyar Antatika: Nahiyar Antatica shine waje mafi tsananin sanyi a duniya domin kuwa ance wajen kowane lokaci yana rufe da dusar kankara, haka kuma wajen nada nauyin gaske don haka saboda wannan dalilai dole sai jirgi yayi kewaye marar amfani kafin ya ketare wajen don haka matukar jirgi sama yabi ta wajen zai iya hadari.



3) Bermuda Triangle: Shekaru masu yawa bayanai sun tabbatar da cewa jiragen sama da dama sun bata a wannan waje kamar sihiri, don haka jiragen sama basa bi ta wajen saboda rash in sanin dalilin hakan.



4) Fadar Buckingham:  wannan itace babbar fadar kasar birtaniya kuma hedikwatar sarauta inda ake gudanar da mulki. Wannan fada ba'a yarda da kowane jirki ya wuce ta samanta ba saboda a tabbatar da tsaron wajen.



5) Wajen shakatawa na Disney Theme: Wannan waje na daga cikin sihirtattun wuraren shakatawa masu matukar ban sha'awa, wannan waje yawanci mutane daga wurare kan ziyarce shi don shakatawa, hakazalika mutane masu haska fina-finai kan je wajen domin daukar film. Wannan waje an hana kowane jirgi giftawa ta samansa saboda kaucewa samun matsala tare da tabbatar da tsaron masu ziyartar wajen. Wannan Waje na tsakanin Florida da California dake Kasar America.



Comments

3 comments
Post a Comment
  1. Tunda de, ba Buhari, zai saya a shugaban kasa ba, Alhamdulillah.

    ReplyDelete
  2. Tudade ba shi ba to yasa kagama

    ReplyDelete
  3. مشاءالله صحه صحوركم يا جمع

    ReplyDelete

Post a Comment